15 Agusta 2016 - 12:26
Sojojin Kasar Masar Ukku Ne Suka Rasa Rayukansu A Wani Harin Ta'addanci A Yankin Sina

Sojojin kasar Masar 3 ne aka tabbatar da mutuwarsu a yankin Sina ta arewa sanadiyyar harin ta'addanci.

Sojojin gwamnatin kasar Masar ukku ne aka tabbatara da mutuwarsu bayan tashin wani bom a safiyar yau litinin a arewacin yankin Sina.

Shafin yanar gizo na labaran Africa Time ya nakalto jami'an tsaron kasar ta na bayyana haka a yau Litinin, ya kuma kara da cewa harin ta'addancin ya aukune a garin Al-magfir dake yankin Sina ta Arewa , sannan wasu mutane biyu ne suka ji rauni a harin. 

Wata majiyar ta kara da cewa bom din irin wadanda ake danawa a gefin titi ne ya tashi da motar sojojin wadanda suke wacewa kusa da wurin. Wata kungiyar yan ta'adda wacce ake kira Ansaru baitil Mukaddasi ce ake tuhuma da tada bon din . Kuma a cikin yan kwanakin da suka gabata kungiyar ta shelanta samar da 'yntacciyar kasar Sina daga kasar Masar.

Gwamnatin kasar Masar dai ta dauri anniyar yakar kungiyoyin yan ta'adda da suke rikita harkokin tsaro a yankin na Sina.288